Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'fajr: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 89 a Mushafi, ayoyi 30, tana farawa a shafi na 593.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura AlgashiyahSura Al'balad ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Inã rantsuwa da alfijiri.

2. Da darũruwa gõma.

3. Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.

4. Da dare idan yana shũɗewa.

5. Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?

6. Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?

7. Iramawa mãsu sakon[1] ƙĩrar jiki.

[1] Tsawo mai ma'ana.

8. Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).

9. Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi[1] suka yi gidãje)?

[1] Wãdil-ƙura, sunan wuri ne kusa da Madina wajen Syria, wato Sham.

10. Da Fir'auna mai turãku.

11. Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?

12. Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.

13. Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.

14. Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.

15. To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."

16. Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."

17. A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!

18. Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!

19. Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.

20. Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.

21. A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.

22. Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu.

23. Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!

24. Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"

25. To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.

26. Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa.

27. Yã kai rai mai natsuwa!

28. Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).

29. Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyi Na (mãsu bin umurui a dũniya).

30. Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura AlgashiyahSura Al'balad ›