Sura ta 104 a Mushafi, ayoyi 9, tana farawa a shafi na 601.
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1. Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
2. Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
3. Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
4. A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
5. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
6. Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
7. Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
8. Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu.
9. A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.
Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)
Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.