Sura ta 113 a Mushafi, ayoyi 5, tana farawa a shafi na 604.
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1. "Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"
2. "Daga sharrin abin da Ya halitta."
3. "Da sharrin dare, idan ya yi duhu."
4. "Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri"
5. "Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada."
Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)
Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.