Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Alkafiroun: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 109 a Mushafi, ayoyi 6, tana farawa a shafi na 603.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'kautharSura Al'nasr ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"

2. "Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba."

3. "Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba."

4. "Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba."

5. "Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake[1] bautã wa ba."

[1] Ãya ta 4 da ta 5 sun nũna addinin ƙarya yakan canza amma na gaskiya bã ya canzawa.

6. "Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni."

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'kautharSura Al'nasr ›