Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'qari'ah: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 101 a Mushafi, ayoyi 11, tana farawa a shafi na 600.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'adiyatSura Al'takathur ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!

2. Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?

3. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?

4. Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.

5. Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.

6. To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.

7. To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.

8. Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).

9. To, uwarsa Hãwiya ce.

10. Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?

11. Wata wuta ce mai kuna.

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'adiyatSura Al'takathur ›