Tambarin TartilTartilRediyo kai tsaye

Sura Al'a'ala: rubutu da fassarar ma'anoni

Sura ta 87 a Mushafi, ayoyi 19, tana farawa a shafi na 591.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'dariqSura Algashiyah ›

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

1. Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.

2. Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.

3. Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).

4. Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.

5. Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.

6. Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.

7. Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.

8. Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.

9. Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.

10. Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.

11. Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,

12. Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.

13. Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.

14. Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.

15. Kuma ya ambaci sũnan[1] Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.

[1] Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran.

16. Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.[1]

[1] Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira.

17. Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.

18. Lalle ne, wannan[1] yanã a cikin littafan farko.

[1] Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko.

19. Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.

Fassarar ma'anoni: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi, bugu na 1.2.2, an wallafa ta daga QuranEnc.com ba tare da wani canji ba. (QuranEnc.com)

Fassara tana isar da ma'anonin Alƙur'ani ne kawai; ba ita ce Alƙur'ani kansa ba. Alƙur'ani shi ne rubutun Larabci da ke sama.

Saurari karatuttukantaKaranta wannan surar a Mushafi tare da tafsiri‹ Sura Al'dariqSura Algashiyah ›